fbpx
Monday, May 10
Shadow

Yan sanda sun bazama farautar wasu mutane wadanda suka azabtar da tsohuwa mai shekaru 98 bisa zargin ta da maita a Jihar Delta

 

Rundunar ‘yan sanda reshen Delta ta fara farautar mutanen da suka addabi wata mata mai suna Misis Margaret Okpole, yar shekaru 98 da ake zargi da maita a garin Otor-Iyede, da ke karamar Hukumar Isoko ta Kudu a jihar.

An bayyana cewa tsohuwar a halin yanzu tana cikin mawuyacin hali, firgita da kuma shan magani a wani asibiti da ba a bayyana ba bayan dangin ta sun azabtar da ita a ranar Juma’a, 19 ga Maris.

An bayar da rahoton cewa wasu yan uwanta da aka ambata da suna; Wada Okpole, Sunday Pada, Jerry Okpole, Emonana Okpole, Egbe Aluya, Oghenemaro, da sauransu, su ne suka shirya wannan mummunan lamarin, kuma dukkansu ‘yan asalin Otor-Iyede ne.

A cikin wani faifan bidiyo da aka yada a yanar gizo, an ga Misis Okpole da wata mata, wasu matasa sun yi musu bulala tare da azabtar da su a gaban wani gida. Dukansu daga baya an jawo su cikin gidan kuma an rufe ƙofar.

Kakakin rundunar, DSP Bright Edafe, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai a ranar Asabar, 24 ga Afrilu, ya ce rundunar ta fara aiki ne bayan da ta samu koke daga Misis Alice Jete, diyar tsohuwar.

DSP Edafe ya ce duk da cewa wadanda ake zargin a halin yanzu sun gudu, amma jami’an rundunar za su zakulosu a duk inda suka boya cikin kankanin lokaci.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *