fbpx
Monday, October 25
Shadow

Yan sanda sun cafke barayin shanu uku a Adamawa, sun kwato bindigogi da shanu

Jami’an rundunar ‘yan sandan jihar Adamawa sun cafke barayin shanu guda uku tare da kwato bindigogi biyu da aka kirkira a cikin gida, shanu biyu daga hannunsu.

Mai magana da yawun rundunar, DSP Suleiman Nguroje, a cikin wata sanarwa a ranar Talata, 12 ga watan Oktoba, ya ce wadanda ake zargi sun shiga hannu ne daga jami’an hukumar leken asiri ta jihar da kuma ‘yan banga na kungiyar Pulaku yayin da suke sintiri sosai a kan Mayo-Belwa da karamar hukumar Fufore don tabbatar da tsaro.

Nguroje ya bayyana sunayen wadanda ake zargin a matsayin Ahmadu Usman mai shekaru 27, mazaunin Wuro Gombe, karamar hukumar Mayo-Belwa, Umaru Jauro Bobbo, 20, mazaunin kauyen kauramai, karamar hukumar Mayo-Belwa da Umar Sahabo, 22, mazaunin Gengle kauyen, karamar hukumar Mayo-Belwa.

Kwamishinan yan sandan Jihar, Mohammed Ahmed Barde ya bada umurnin cigaba da bincike akan wadanda ake zargin.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *