fbpx
Wednesday, June 23
Shadow

Yan sanda sun cafke masu garkuwa da mutane 10, tare da kwato bindigogi, da alburusai a Enugu

Rundunar ‘yan sanda a Enugu ta ce jami’an‘ yan sanda da ke aiki da ‘Operation Restore Peace’ sun cafke wasu masu laifi 10 da ake zargi da satar mutane, fashi da makami, mallakar bindiga ba bisa ka’ida ba da kuma fada a jihar.

Jami’an sun kwato bindigogi biyu, harsasai masu rai hudu, da motoci biyu, da babura uku, da adda da dai sauran abubuwa.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sanda na jihar, ASP Daniel Ndukwe, ya bayyana a cikin wata sanarwa a ranar Alhamis a Enugu cewa, wannan abin da ya faru domin bin umarnin “ Operation restore peace ‘ ‘ne.
Ndukwe ya ce, “A ranar 28 ga Mayu da misalin karfe 7 na safe,‘ yan sanda da ke hade da sashin ’yan sanda na Nimbo tare da hadin gwiwar kungiyar masu lura da unguwanni suka cafke Nnamdi Okweli, mai shekaru 26; Victor Nwakor, 23 da Chisom Nwankpa, 22 da sauransu ake zargi da yin garkuwa, fashi da makami da yin fada, yayin da wasu suka tsere.
Ya ce kwamishinan ‘yan sanda na jihar, Mista Mohammed Aliyu, ya sake tabbatar da jajircewar rundunar don aiwatar da ayyukan’ Operation restore peace’.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *