fbpx
Thursday, September 23
Shadow

Yan sanda sun cafke mutane 4 da ake zargi’ yan fashi ne a Kogi

Rundunar ‘yan sanda a Kagi, ta cafke wasu mutane hudu da ake zargin’ yan fashi da makami ne, wadanda suka addabi mazauna karamar hukumar Bassa ta jihar.

Kakakin rundunar, William Aya, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis.

Mista Aya ya bayyana cewa an kama wadanda ake zargin ne bisa rahoton sirri da aka samu a wani gida da ke sabon Jerusalem Oguma a karamar hukumar Bassa.

Mista Aya ya bayyana sunayen wadanda ake zargin; Guda Dangana, Dogo Chure, Dekina Zhiya da Samson Nyiza, ya kara da cewa an samu karamar bindiga, harsasai guda da kuma kokon kan mutum guda biyu.

A cewarsa, za a gurfanar da wadanda ake zargi a gaban kotu bayan bincike.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *