fbpx
Thursday, September 23
Shadow

Yan sanda sun cafke mutane 8 da ake zargi da kisan baban tsohon gwamnan Filato

 

Rundunar ‘yan sanda a ranar Laraba ta ce ta cafke mutane takwas da ake zargi da garkuwa da kashe Defwan Dariye mai shekaru 93, mahaifin tsohon gwamnan Filato, Joshua Dariye.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar, Frank Mba, ne ya bayyana hakan yayin ganawa da manema labarai a Abuja.

A cewarsa, bayan tattaunawa mai tsawo, an biya kudin fansa na Naira miliyan 10 ga masu garkuwar kuma a maimakon su sake shi, sai suka kashe shi.

Mista Mba ya ce lamarin ya faru ne a watan Yunin 2020, inda ya kara da cewa bayan sun dawo da gawar mamacin, sashin bincike na yan sanda sun shiga aiki don gano wadanda suka aikata laifin.

A cewarsa, an cafke wadanda ake zargin ne bayan da Jami’an Rundunar Leken Asiri suka kai wani samamen bayan samun bayanan sirri.

Mista Mba ya ce an kwato AK47 guda 26, riffle AK49 guda daya da kuma harsasai 14 na bindigar AK47, daga hannun wadanda ake zargi.

Ya kuma ce za a gurfanar da wadanda ake zargin a gaban kotu bayan an kammala bincike.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *