fbpx
Monday, May 10
Shadow

Yan sanda sun cafke tsohon mai laifin da ya saci wayoyi 273 da kudin su ya kai N15m a Katsina

Rundunar ‘yan sanda reshen jihar Katsina ta cafke wani shahararren barawo kuma tsohon mai yanke hukunci tare da kwato wayoyin hannu 273 da kudinsu ya kai N15m.

Kakakin rundunar, SP Gambo Isah, wanda ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa a ranar Juma’a 30 ga Afrilu, ya ce wanda ake zargin, Ibrahim Lawal, kwararre ne kan fasa gida da satar babura.

A yayin gudanar da bincike, an gano wayoyin salula na GSM dari biyu da saba’in da uku (273) a hannun sa yayin binciken ‘yan sanda.

Wanda ake zargin ya amsa laifin kuna za a gurfanar da shi a gaban kotu da zarar an kammala bincike.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *