fbpx
Tuesday, May 11
Shadow

Yan Sanda sun cafke wani dan Arewa a Jihar Osun bisa zargin satar mutane

yansanda sun damke wani matashi dan shekaru 20, mai suna Ahmad Muhammad da ake zargi da satar mutane a Jihar Osun.

 

Matashi ya fadawa rundunar ‘yan sanda ta jihar Osun cewa ya yanke shawarar zama a kusa da manyan hanyoyi ne domin da shi da sauran mambobin kungiyar sa su dinga yin garkuwa da mutane cikin sauki.

 

An kama Muhammad, wanda ya fito daga garin Tambuwal a jihar Sokoto, a Wasinmi, wani kauye da ke kan babbar hanyar Ife zuwa Ibadan.

 

Yayin da ake gabatar da shi a hedikwatar ‘yan sanda da ke Osogbo, babban birnin jihar, Muhammad ya ce shi memba ne na gungun mutane bakwai na masu satar mutane da suka sace fasinjoji a kan babbar hanyar, ya kara da cewa an kama shi ne yayin wata musayar wuta da‘ yan sanda.

 

Yace yayi bakin ciki matuka irin yanda sauran membobin suka gudu suka bar shi a dajin.

Ya kara da cewa dole ne yan sanda su cafke shi cikin sauki saboda bai san hanyoyin da ke cikin wannan daji ba, balle yabi sawun su har zuwa inda suke.

Ya ce sauran mambobin kungiyar Fulani ne kuma ya ba da sunayensu kamar Alhaji, Buba, Siraju, Sadiq, Saidu.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *