fbpx
Sunday, September 19
Shadow

Yan sanda sun cafke wani direba bisa zarginsa da shirya fashi da makami ga fasinjojinsa a Jigawa

Jami’in hulda da jama’a na ‘yan sanda ASP Lawan Shiisu Adam ya tabbatar da hakan ga manema labarai a Dutse, babban birnin jihar.

Adam ya bayyana cewa lamarin ya faru ne bayan fasinjoji shida sun shiga wata motar kasuwanci ta Peugeot citron 897 tare da lamba KNS 572 TRN a zagayen NNPC da ke kano zuwa ƙauyen Babaldu a cikin karamar hukumar B / Kudu.

Ya ce a lokacin da suka isa Tsamiyar Tannaga kan iyaka tsakanin Kano da Jihar Jigawa wasu mutane da ba a san su ba wadanda ke tsaye a bakin hanya suka yi wa direban magan domin ya tsaya.

Ya ce, fasinjojin, sun gargadi direban da kar ya tsaya a daidai wurin da daddare amma direban ya yi biris da su sannan ya ajiye motarsa.

Kakakin ‘yan sandan ya ce nan da nan direban ya tsaya, wasu mutane hudu da ba a san su ba dauke da sanduna da adduna fuskokinsu rufe sun fito daga daji suka yi musu fashin kudi na Naira dubu dari da casa’in da biyar (195,000.00).

Wadanda lamarin ya rutsa da su sun kai rahoton lamarin ga ‘yan sanda bayan da suka yi zargin direban ya kasance babban jagoran harin na su.

An kama direban mai suna Yahya Muhammad na kauyen Kangire a karamar hukumar B / Kudu.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *