fbpx
Wednesday, June 23
Shadow

Yan sanda sun cafke wani manomi da ya sanya guba a rijiyoyi 9 don cutar da makiyaya dake shiga gonarshi a jihar Yobe

An kama wani manomi mai shekaru 25, Mohammad Mohammad a kauyen Kasesa kusa da Damaturu a jihar Yobe bisa zargin sa guba a rijiyoyi tara a cikin al’umma.
Rundunar ‘yan sandan jihar, ta bakin kakakinta, ASP Dungus Abdulkarim ta tabbatar da kamun a ranar Alhamis a wata hira da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN).
Kakakin ya ce wanda ake zargin ya amsa aikata laifin amma ya ce yana da niyyar hana makiyaya shiga gonarsa ne.
PPRO ya kuma bayyana cewa rundunar tana kokarin ganin ta cafke makiyayan wadanda suka yi zargin sun mamaye gonar wanda ake zargin.
Kakakin ya bukaci manoma da makiyaya da su kauce daga ayyukan da ka iya haifar da rikici a jihar.
”A ranar 25 ga watan Mayu, ya zuba maganin kwari a cikin rijiyoyi tara wadanda su ne hanyoyin samun ruwa ga mazauna da garken yankin.
“A lokacin da muka tattara ruwan rijiyar a matsayin samfurin kuma muka gudanar da bincike a dakin gwaje-gwaje, mun gano cewa sun gurbace da wasu sunadarai,  wadanda za su iya haifar da cutar kwalara, taifot da sauran cututtukan da ke dauke da ruwa.
“Saboda haka, mun gano kuma mun kama wanda ake zargin a yau. Za a gurfanar da shi a kotu ba da jimawa ba, ”in ji Abdulkarim.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *