fbpx
Saturday, April 17
Shadow

Yan sanda sun cafke wata mata dake kokarin sayar da jaririnta N40,000 a Jihar Ebonyi

Rundunar ‘yan sanda reshen jihar Ebonyi ta kama wata karuwa mai suna, Victoria Chukwube bisa zargin ta da shirin sayar da jaririnta a kan kudi N40,000.

Jaririn wanda bai wuce wata huɗu da haihuwa ba kuma har yanzu yana sha nono.

Dalilinta kuwa shi ne ta tara kudade domin bude shagon sayar da giya saboda bata da halin daukar nauyin jaririn nata.

Da yake yi wa manema labarai bayani a hedikwatar rundunar da ke Abakiliki, jami’in hulda da jama’a na ’yan sanda, DSP Loveth Odah ya ce an kama matar ne a ranar Juma’ar da ta gabata bayan wani mutum ya samu labarin, kuma nan take ya sanar da Hukumar.

Ya kuma ce za’a cigaba da bincike kafin a dauki mataki na gaba.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *