fbpx
Thursday, August 5
Shadow

Yan sanda sun ceto mutum shida da aka yi garkuwa da su, tare da mutane biyu da ake zargi a Jihar Edo

Jami’an rundunar ‘yan sandar Edo sun ceto mutum shida da aka yi garkuwa da su a kan hanyar Benin-Ekpoma.

Kakakin rundunar, Kottongs Bello, wanda ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa a ranar Alhamis, 8 ga watan Yuli, ya ce an kuma kama wasu mutane biyu da ake zargin masu satar mutane ne.

PPRO ya ce biyu daga cikin masu garkuwan sune, Abdulkarim Kazeem, mai shekaru 40 da Odoh Chukchekua, mai shekaru 40, an kamasu a yayin gudanar da aikin yayin da wasu suka tsere da raunukan bindinga.

Rundunar ta gargadi masu aikata laifuka a cikin jihar Edo da su tuba ko su yi kaura daga jihar ko kuma a kamasu tare da fuskantar fushin doka.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *