fbpx
Sunday, April 18
Shadow

Yan sanda sun ceto wata yarinya daga hannun masu garkuwa da mutane tare da cafke mutane 2 da ake zargi

Rundunar yan sanda ta Jihar Benuwai mai suna ‘Operation Zenda’ sun ceto wata yarinya ‘yar shekaru 13’ yan awanni kadan bayan wasu ‘yan daba sun sace ta a karamar hukumar Kwande da ke jihar.

An bayyana cewa an sace yarinyar mai suna Mngusuur Iorlian da misalin karfe 12 na daren ranar Lahadi, 4 ga Afrilu, daga gidan mahaifinta, wanda ke kusa da NKST Church, Akpera a Adikpo.

Bayan samun bayanan, sai jami’an “Operation Zenda” suka bi sawun wadanda ake zargin zuwa maboyarsu a yankin Mbawer, Kwande, inda suka kubutar da yarinyar.

An kama daya daga cikin wadanda ake zargin mai suna Vershima Sunday tare da wata mai suna Grace Yaaor.

Sauran mutane hudu sun tsere yayin da maharan suka kwato wani babur da ‘yan kungiyar suka yi amfani da shi.

Kwamandan Operation Zenda, CSP Justine Gberindyer ya gargadi masu satar mutane da su bar Benuwai, saboda ba za sake samun kwanciyar hankali a Jihar ba.

A halin yanzu, mai magana da yawun rundunar, DSP Catherine Anene, wacce ta tabbatar da faruwar lamarin ta ce ‘yan sanda na bin diddigin wadanda suka gudu, inda ta kara da cewa yarinya da aka kubutar ta hadu da iyayenta.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *