fbpx
Monday, September 27
Shadow

Yan sanda sun fara bincike kan kisan gillar da aka yiwa ma’aikacin NTA a Kogi

Rundunar ‘yan sandan jihar Kogi ta fara gudanar da bincike don gano yanayin da ya kai ga mutuwar ma’aikacin gidan talabijin na Najeriya, (NTA).

Marigayin mai suna Onwukwe Chukwu Obiahu, jim kadan bayan ya tashi daga aiki a daren Talata, 7 ga watan Satumba, wasu mutane da ba a san ko su waye ba, sun farmasa inda sukai sanadiyyar mutuwarsa.

An tattaro cewa an tsinci gawar marigayi Obiahu wanda ke aiki a sashin injiniyoyi na tashar bola ta NTA a Okene a hanyar Okene Ogori Magong a safiyar ranar Laraba, 8 ga watan Satumba.

An kuma kara da cewa an kama dukkan ma’aikatan da ke bakin aiki kuma a halin yanzu ana yi musu tambayoyi a ofishin sashin rundunar ‘yan sandan Najeriya da ke Okene.

Wani ma’aikacin NTA a Okene da ba ya son a ambaci sunansa ya tabbatar wa da jaridar Nigerian Tribune faruwar lamarin.

Kakakin rundunar, DSP William Ovye Aya, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin ya ce rundunar ‘yan sandan ta fara gudanar da bincike da nufin gano musabbabin mutuwarsa, kamawa tare da gurfanar da masu laifin a gaban kuliya.

A halin da ake ciki, Kungiyar ‘Yan Jaridu ta Najeriya, (NUJ), ta yi Allah wadai da kisan gilla da aka yi wa injiniyan NTA.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *