fbpx
Tuesday, August 3
Shadow

Yan sanda sun harbe wani dan fashi da makami a kan babbar hanyar Jihar Ogun

ll

Yan sandan jihar Ogun sun harbe wani dan fashi da makami a kan hanyar Shagamu / Ijebu ode dake Jihar, yayin da suke yiwa mutane fashi.

Wata sanarwa da DSP Abimbola Oyeyemi, mai magana da yawun rundunar ‘yan sanda na jihar, ya ce wanda ake zargin ya hadu da ajalinsa ne lokacin da DPO Odogbolu, SP Awoniyi Adekunle da mutanensa da ke aikin sintiri tare da wasu sojoji, suka samu kiran gaggawa cewa wasu ‘yan fashi da makami da yawansu ya kai kimanin bakwai sun tare hanyar da ke kusa da jami’ar kudu maso yamma, kuma suna kwace kayayyakinsu.

A karshen artabun, an cafke daya daga cikin ‘yan fashin da munanan raunuka yayin da wasu suka tsere da raunuka daban-daban na harbin bindiga, wanda akan hanyar zuwa asibiti ya mutu.

Oyeyemi ya kara da cewa kwamishinan ‘yan sanda Cp Edward Awolowo Ajogun, wanda ya yaba da saurin amsa kiran gaggawa da jaruntakar mutanen sa sukai, ya kuma ba da umarnin cewa a yiwa yankin kawayan domin cafke mambobin kungiyar da suka tsere.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *