fbpx
Tuesday, May 18
Shadow

Yan sanda sun kama mutane 18 da ake zargi da hakar ma’adinai ba bisa ka’ida ba a Jihar Zamfara

Hukumar ‘yan sanda ta cafke wasu mutane 18 da ake zargi da hakar ma’adinai ba bisa ka’ida ba a karamar hukumar Maru da ke jihar ta Zamfara.

Kamun ya biyo bayan umarnin shugaban kasa na hana hakar ma’adanai ba bisa ka’ida ba a jihar.

Kakakin rundunar ‘yan sanda na jihar, SP Shehu Muhammad, ya ce kungiyar masu yaki da hakar ma’adinai ba bisa ka’ida ba, karkashin jagorancin SP Murtala Bello, sun fara wani samame da kakkabe masu hakar ma’adanai a wurare daban-daban a fadin jihar.

Ya ce rundunar ta ci gaba da gudanar da ayyukanta tun daga watan Satumbar shekarar 2020 lokacin da suka kai samame wurare daban-daban da ake hakar ma’adanai ba bisa ka’ida a cikin jihar kuma suka yi nasarar kame wasu masu hakar ma’adanai ba bisa ka’ida ba.

A karshe, ya yi gargadin cewa wadanda ke yin hakar ma’adanai ba bisa ka’ida ba su guji aikata hakan, ya kara da cewa sojoji ba za su yi kasa a gwiwa ba wajen cafke duk wanda aka samu da laifi.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *