fbpx
Monday, November 29
Shadow

Yan Sanda Sun Kama Wani Da Ake Zargin Ya Baiwa Makwabcinsa Zakani Ya Sha Ya Mutu A Abuja

’Yan sanda a garin Zuba da ke yankin Birnin Tarayya, Abuja sun kama wani mai suna Muhammad Lawan bisa zarginsa da hannu a rasuwar makwabcinsa da ake zargin ya ba shi ’ya’yan itacen zakami ya ci a matsayin magani.

Wanda ake zargin da marigayin mai suna Ibrahim Rabo makwabta ne a Kasuwar Kayan Marmari ta Abuja da ke garin Zuba, inda suke kasuwanci tare da kuma kula da wani masallaci.
An yi jana’izar mamacin a ranar Talatar da ta gabata bayan jinya na kwana biyu.
Wani da waklinmu ya zanta da shi a kasuwar, ya ce wanda ake zargin na kula da tsiron zakami da ke gefen wani kwari ne a kusa da kasuwar ta hanyar tattalinsa da kuma ba shi ruwa.
Haka  wakilinmu ya ga lokacin da aka kawo wanda ake zargin ofishin ’yan sanda na Zuba inda ake ci gaba da tsare shi. Sai dai a bayanin da ya yi, ya musanta zargin ba marigayin maganin da hannunsa. Ya ce ya ciro kwallon zakamin ne a kusa da kwarin inda ya je fitsari. “To bayan na gama ne sai na yi sha’awar itacen na balli kwallonsa na dawo da shi.
“Na ajiye shi a kan katanga sai aka samu akasi, shi kuma ya dauka ya bantari kadan daga jikin kwallon har wannan lamari ya faru,” inji shi.
Majiyarmu ta samu labarin cewa da farko marigayin ya fitar da suturar da ke jikinsa tare da shiga dimuwa tun a ranar farkon lamarin. Bayanin ya ce daga bisani an killa ce shi a wani waje tare da sanya masa ruwan magani.
Babban Jami’in ’Yan sandan Zuba, CSP Muhammad Yahaya wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce za su mika mutumin ga hedikwatarsu a Abuja da zarar sun kammala binciken farko.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *