fbpx
Thursday, August 5
Shadow

Yan sanda sun kara ceto wasu daliban makarantar Baptist biyu a jihar Kaduna

Jami’an ‘yan sanda a Kaduna sun ceto biyu daga cikin daliban makarantar sakandaren da aka sace na Bethel Baptist da ke karamar hukumar Chikun ta jihar.

An ceto daliban ne a yankin Rijanna da ke kan hanyar Kaduna zuwa Abuja, da yammacin Laraba.

Yayin da yake tabbatar da faruwar lamarin, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna, ASP Mohammed Jalige ya ce an kai daliban asibitin likitoci don duba lafiyarsu.

Tare da wannan ci gaban, yanzu haka daliban guda 118 suna hannun yan bindiga kamar yadda aka gano wata dalibar a cikin makon da ya gabata.

An rahoto cewa yan fashin sun bukaci a basu kudin fansa naira miliyan 60 kafin su sako sauran daliban.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *