fbpx
Sunday, April 18
Shadow

Yan sanda sun kashe wani dan bindiga, tare da kwato bindigar Ak-47 a jihar Neja

Rundunar ‘yan sandan Neja ta harbe wani dan fashi har lahira tare da kwato bindiga kirar AK-47 guda daya daga hannun shi a kauyen Tashan – Barau da ke karamar hukumar Rafi ta jihar.
Mista Adamu Usman, kwamishinan ‘yan sanda a jihar, ya bayyana hakan a wata hira da manema labarai a Minna ranar Laraba, NAN ta ruwaito.
Usman ya bayyana cewa jami’an rundunar sun yi aiki da wani sirri wanda ya nuna cewa an hango wasu gungun ‘yan fashi a kan babura suna zuwa Pangu-Gari da ke karamar hukumar Rafi.
Ya ce rundunarsu sun tattara zuwa wurin kuma sun yi artabu da ‘yan bindigar a ƙauyen Tashan-Barau, a kan hanyar Tegina zuwa Minna.
A cewarsa, an harbe daya daga cikin ‘yan fashin wanda daga baya aka bayyana sunansa da Mohammed Garba na Ungwan Sani, yankin Sabon Mariga da ke karamar hukumar Rafi, yayin da aka gano bindiga kirar AK 47 da babur din Bajaj da ba shi da rajista.
Kwamishinan ya ce an ijiye gawar mai laifin a dakin ijiye gawarwaki na asibiti.
Ya tabbatar wa jama’a cewa rundunar za ta ci gaba da kai hare-hare a kan ‘yan ta’addan sannan ya yi kira ga mazauna da su ba da bayanai masu amfani da lokaci ga jami’an tsaro.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *