fbpx
Wednesday, May 12
Shadow

Yan sanda sun kashe yan bindiga shida a Shiroro, jihar Neja

Yan sanda a jihar Neja sun kashe’ yan bindiga shida yayin artabun da aka yi a Garkogo, karamar hukumar Shiroro ta jihar.
Da yawa daga cikin ‘yan fashin, sun tsere da munanan raunuka na bindiga, sun bar baburarsu.
‘Yan sandan wadanda aka girke a garin Garkogo bayan ci gaba da kai hare-hare daga yan ta’addan a cikin ‘yan kwanakin nan.
Yan bindigan sun harbe wani dan kauyen har lahira kafin’ yan sanda su bayyana a wurin kuma suka yi artabu da su da misalin karfe 3:30 na safiyar ranar Asabar.
Wannan nasarar na zuwa ne kusan makonni uku bayan da wasu ‘yan bindiga suka kai hari a sansanin jami’an tsaro tare da kashe sojoji biyar da wani jami’in tsaro na farin kaya a Allawa.
Wata majiya a Garkogo ta shaida cewa hudu daga cikin ’yan fashin an kashe su nan take yayin da aka tsamo gawarwakin wasu biyu daga wata gona da rana, wadanda suka mutu sakamakon raunin harbin bindiga.
Majiyar ta kara da cewa babu wani wanda ya jikkata a bangaren ‘yan sandan.
Kokarin jin ta bakin rundunar ‘yan sanda na jihar ya ci tura saboda ba a samu jin ta bakin jami’in hulda da jama’a, DSP Wasiu Abiodun ba har zuwa lokacin hada wannan rahoton.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *