fbpx
Tuesday, May 18
Shadow

Yan sanda sun tabbatar da sace wasu daliban jami’ar tarayya Uku a jihar Benue

Rundunar ‘yan sanda a Benuwai ta tabbatar da sace wasu dalibai uku na Jami’ar Aikin Gona ta Tarayya, Makurdi, da wasu‘ yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sukayi.
Mai magana da yawun ‘yan sanda a Benuwe, DSP Catherine Anene, ta shaida wa manema labarai cewa an sace daliban ne da misalin karfe 10.20 na daren Asabar yayin da suke karatu kusa da zauren makarantar.
Ta tabbatar da cewa an fara gudanar da cikakken bincike a kan lamarin, tare da fatan gano masu garkuwar.
“An samu bayanai daga hukumar makarantar a ranar 24 ga Afrilu, da misalin karfe 10.20 na dare, cewa wasu mutane da ba a san su ba sun sace wasu dalibai uku da ke karatu.
“Mun samu wannan bayanin kuma muna kan sa. Za mu ci gaba da yin iya kokarin mu don ganin mun kai ga tushen wannan laifin.
“A yanzu, shawarata ga iyayen daliban ita ce su kwantar da hankulansu. Muna iyakar kokarinmu don ganin sun dawo da yaransu, ’’ in ji ta.
Anene, duk da haka, ta ƙi yin bayani kan ko masu garkuwar sun tuntubi hukumomin makarantar ko iyayen waɗanda aka sace ko a’a.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *