fbpx
Wednesday, January 26
Shadow

‘Yan sanda za su fara kamen masu daukar amarya>>DSP Kiyawa

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano za ta fara kamen ba sani ba sabo akan duk direbobin adaidaita sahun da ta samu su na guje-guje da sunan daukar amarya a lokacin bukukuwa.

Mai magana da yawun rundunar DSP Abdullahi Haruna kiyawa ne ya bayyana hakan a ganawarsa da gidan Rediyon Dala a yau Talata.
Ya kuma ce, “Doka ba za ta bari a ringa ganganci da ababan hawa ana hallaka rayuwar al’umma ba.”  A cewar Kiyawa


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Ya kara da cewa, “Duk wanda aka samu a cikin baburin shima ya na da laifi, domin haka doka ba za ta bar shi ba.”

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Kano D.S.P. Abdullahi Haruna kiyawa ya kuma shawarci magidanta da su gargadi matayensu kan hawa irin wadannan Babura a lokutan biki, don kaucewa fadawa hannun hukuma.
DalaFM


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *