fbpx
Tuesday, June 15
Shadow

Yan sandan Jihar Kogi sun kashe masu satar mutane 2 a musayar wuta

Tawagar ‘yan sanda masu yaki da masu aikata laifuka a Kogi sun fatattaki wasu mambobi biyu na wasu mutane biyar da ake zargin masu satar mutane ne a musayar wuta a babbar hanyar Ajaokuta.

Onogwu Muhammed, Babban Sakataren yada labarai na gwamnan Kogi, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya raba wa manema labarai ranar Laraba a Abuja.

Mista Muhammed ya ce ‘yan sanda sun fatattaki wannan kungiyar masu garkuwa da mutane da ke sanye da kayan sojoji.

Ya ce, rundunar ta ‘yan sanda ta kuma kwato makamai, kudi, wayoyi, katin ATM na banki da sauran kayayyaki daga hannun masu laifin.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *