fbpx
Thursday, July 29
Shadow

Yan Sandan Kano Sun Kama Wasu Mutane 10 Da Suka Kwarewa Wajen Kutsen Asusun Bankunan Mutane

Yan sanda da ke aiki a rundunar’ yan sanda ta Jihar Kano sun kame akalla maza takwas da mata biyu bisa zargin su da kasancewa cikin kungiyar masu aikata laifi yin kutse a asusun bankunan mutane don cire masu kudi.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar, DSP Abdullahi Haruna-Kiyawa, shine ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai a jihar Kano.

Kakakin rundunar ya bayyana cewa wadanda ake zargin sun amsa laifukansu na yin kutse a asusun bankunan mutum daban-daban tare da cire kudade masu yawa.

Kwamishinan ‘yan sanda, Mista Sama’ila Shu’aibu-Dikko, ya bayyana cewa ya ba da umarnin gudanar da bincike cikin hankali a kan lamarin.

Ya kara da cewa babu wani abu da ya rage illa su gurfanar da su a gaban kotu.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *