fbpx
Monday, November 29
Shadow

‘Yan Shi’a Sun Cika Tituna a Abuja bayan dage Shari’ar Sheikh Zakzaky

Bayan zaman kotun da aka gudanar yau wanda babba kotun Kaduna ke sauraron karar da Jihar Kaduna ta shigar da Sheikh Zakzaky da Matarsa Mallama Zeenah tana tuhumar su da wasu Laifuka 8 ciki harda kisan kai. Lauyoyin Gwamnati da na Mallam Zakzaky sun fafata sosai a kotu wanda daga karshe alkalin ya sanya ranar 24 da 25 ga watan Febrairu domin cigaba da Shari’ar.

Lauyan dake Wakiltan Gwamnati Barista Bayero Dari, ya nemi kotun data tilasta kawo Mallam Zakzaky yayin Shari’ar Inda Lauya me kare Shekh Zakzaky Barista Femi Falana yaki yarda da hakan da dalilin bayyana cewa Mallam da Malama Zeenah suna fama da rashin lafiya me tsanani.
Mabiya Shi’a Almajiran Malam Zakzaky sun fito a manyan titunan Abuja suna nuna rashin amincewan su da yanda ake tafiyar hawainiya a shari’ar musamman da Mallam Zakzaky da matarsa suke cikin yanayin rashin lafiya na harbin harsashi a jikin su.
Rahotanni sun bayyana cewa sunyi irin wannan fitar a garuruwan Zariya da Katsina.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *