fbpx
Monday, November 29
Shadow

‘Yan ta’adda zasu kawo mummunan hari Najeriya>>Kasar Ingila ta yi gargadi

Kasar Ingila ta yi gargadin cewa, ‘yan ta’adda na shirin kawo wani mummunan hari Najeriya inda ta gargadi ‘yan kasarta kada su je wasu jihohin Najeriya 12.

 

A sanarwar data fitar a shafinta na yanar gizo ranar Juma’a, kasar tace tana gargadin ‘yan kasarta dake Najeriya su rika saka ido suna kuma sauraren kafafan yada labarai na cikin kasa dan sanin halin da ake ciki.

 

Kasar tace akwai kuma alamun za’a yi Zanga-Zanga a fadain Najeriya dan tunawa da Zanga-Zangar EndSARS dan haka tace ‘yan kasarta su kula dan za’a iya samun matsalar tsaro.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

1 Comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *