fbpx
Monday, November 29
Shadow

Yanda aka kaiwa Musulmai munanan hare-hare a India

Har yanzu Ameeruddin na cike da kaduwa sakamakon lalata dan karamin kantin da yake gudanar da kasuwancinsa da aka yi a kauyensu.

Musulmi ne kuma yana zaune lafiya a kauyensu da ke arewacin jihar Tripula da ke Indiya.

Sai dai a watan da ya gabata wasu ‘yan daba mabiya addinin Hindu sun far wa kauyensu.

“Ina tsaye a gefen gonar shinkafa, sai kawai ‘yan daba suka kai hari kasuwar kauyenmu,” in ji shi.

“Tun da babu damar su kai hari gidajenmu saboda ‘yan sanda na wajen, sai suka huce a kan shagunanmu, a lokacin da muka tafi hutun sa’o’i kadan.”

Yana tara ‘yan kudaden da yake samu domin kula da iyalansa, saboda babu wadatattun ayyuka a kauyen Rowa.

Mutum daya cikin goma Musulmi ne a yankin mai al’umma sama da miliyan hudu.

A iya kiransu da tsirarun mutane a yankin mai kewaye da mabiya addinin Hindu.

Yayin da rikicin addini ya zama ruwan dare a wasu yankunan Indiya, kauyen Rowa bai taba fuskantar hakan ba.

‘Yan daban sun fada kauyen da ke makoftaka da Rowa, inda suka kona wani masallaci.

Idan ka shiga ciki, an kakkarya kofofi da tagogi, gilasai sun tarwatse, fankoki ma an karya su.

Gidajen mabiya addinin Hindu da Musulmai ne suka kewaye masallacin Chamtila, amma yanzu mazauna yankin sun gwammace zama a cikin gida.

Jami’an tsaro sun sanar da cewa an kai rahoton barkewar rikicin addini sama da sau 10 a arewacin jihar Tripura a watan Oktoba kadai.

Babban jami’in ‘yan sanda gundumar Bhanu Pada Chakraborty, ya musanta kai hari masallacin, amma ya amince an shiga gidaje da dama a yankin ba tare da fadar adadinsu ba.

Yadda lamarin ya samo asali

An kai harin ne bayan gagarumar zanga-zangar da kungiyar mabiya addinin Hindu mai suna Vishva Hindu Parishad (VHP) ta gudanar ranar 26 ga watan Oktoba, wadda ta hannun damar jam’iyyar BJP mai mulkin Indiya ce.

Sun yi zanga-zangar kin amincewa da harin da aka kai wa mabiya addinin Hindu a makwabciyar kasarsu wato Bangladesh.

An yi zanga-zangar ne a garin Panisagar da ke iyaka, kilomita kadan daga garin su Ameeruddin.

Rahotanni sun bayyana cewa kusan mutum 3,000 ne suka fito zanga-zangar.

“Kusan mutum 10,000 ne suka fito zanga-zangar, kuma mabiya addinan Hindu da Musulunci sun zargi juna da tsokanar fada, muna kuma gudanar da bincike akai,” in ji Mista Chakraborty.

Bijit Roy, shugaban jam’iyyar VHP, ya zargi cewa wadanda suka kai wa Musulmai harin ba ‘yan yankin ba ne.

“Ba ma kin Indiyawa musulmai, ai mutanenmu ne, tare muke zaune, suna da ‘yanci kamar yadda muke da shi,” in ji shi.

“Tarzomar ta fara ne da yada jita-jitar ana jifar masallaci da duwatsu. Ina kokarin kare masallacin ne.” Garin Kadamtala ba shi da nisa Panisagar.

Yayin da aka fara yada jita-jitar a shafukan sada zumunta kan cewa ‘yan daba sun far wa masallatai da shagunan Musulmai suka yi dandazo a Kadamtala.

Sun fara hayaniya da bukatar a yi gaggawar kama wadanda suka yi aika-aikar.

A kauyen Churaibari, mabiya addinin Hindu da ke yankin sun ce suna kai hari ne kan Musulmai.

Iyalan Saha da ke zaune a bene hawa biyu sun nuna mana bidiyon da suka dauka a wayar salula, lokacin da ‘yan daba ke jifan gidan da duwatsu tare da lalata motocin da ke harabar gidan.

Sonali Saha, mai shekara 18, ta ce tun daga ranar ba ta kara yin bacci ba.

“Lamarin ya fara da misalign karfe 10 na dare, lokacin ina karatu, kungiyar ‘yan dabar suka zo tare da jifan gidanmu da duwatsu da kwalabe. Cikin minti 10 zuwa 15 suka gudu, amma tsoro ya hana ni ko motsi. Mahaifiyata ce ta yi kokarin rufe tagogi.”

Daga shekarar 2018 ne jam’iyyar BJP ta fara shugabancin Tripura, bayan shafe shekaru 25 a hannun jam’iyyar Kwamunusanci. ‘Yan adawa sun zargi jam’iyya mai Mulki ta gwamutsa addini da siyasa wuri guda domin su lashe zabe, zargin da BJP ta musanta.

“Ina ganin tsirarun Musulmai da ke zaune a nan suna karkashin kariyar gwamnatinmu. Muna bibiyar duk abin da ke faruwa, kuma ba mu ji dadi ba kana shin hankali na baya-bayan nan,” in ji mataimakin kakakin majalisa Biswa Bandhu Sen mai wakiltar arewacin Tripura.

“‘Yan adawar siyasa ne ke son shafa wa Firaiminista Narendra Modi tun da muna cikin gwamnati da ke wannan yankin.”

Makwanni kadan bayan tarzomar, gwamnatin jihar ta tsare wasu ‘yan jarida biyu, kan laifin yada labaran da suka kara ta’azzara matsalar. Amma daga bisani kotu ta ba da belinsu.

Shugabannin jam’iyyar BJP sun musanta zargin suna take ‘yancin fadar albarkacin baki da hana ‘yan jarida gudanar da ayyukansu.

‘Yan sandan Panisagar sun gayyaci tawagar BBC domin sanin dalilin ziyarar tasu. Sannan duk inda suka sanya kafa ‘yan sand ana biye da su, musamman lokacin da suke tattaunawa da musulmai mazauna kauyen da aka farfasa wa shaguna.

Makwanni kadan bayan tarzomar, gwamnatin jihar ta tsare wasu ‘yan jarida biyu, kan laifin yada labaran da suka kara ta’azzara matsalar. Amma daga bisani kotu ta ba da belinsu.

Shugabannin jam’iyyar BJP sun musanta zargin suna take ‘yancin fadar albarkacin baki da hana ‘yan jarida gudanar da ayyukansu.

Yan sandan Panisagar sun gayyaci tawagar BBC domin sanin dalilin ziyarar tasu. Sannan duk inda suka sanya kafa ‘yan sand ana biye da su, musamman lokacin da suke tattaunawa da musulmai mazauna kauyen da aka farfasawa shaguna.

Kawo yanzu, lamura na komawa yadda suke a yankin, sai dai har yanzu akwai tsoro a zukatan mutane musamman wadanda lamarin ya shafa.

Wadanda aka fasa wa shaguna sun bayyana cewa rayuwa ta yi tsauri, sakamakon wawashe musu dukiya da aka yi.

“Lamarin na da tsauri, to amma yaya za mu yi? Haka nan muka hakura, a hankali muna farfadowa dgaa halin da aka jefa mu a ciki, tare da fatan hakan ba za ta sake faruwa ba, har abada,” in ji Amir Hussain, mai shekara 41, wanda aka fasa wa shago.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *