fbpx
Thursday, September 23
Shadow

Yanda aka kashe dan Bindiga yayin da yake karbar kudin fansa a Adamawa

 

 

‘Yan Bijilante sun kashe wani me garkuwa da mutane a yayin da yake karbar kudin fansa daga hannun dangin wanda akan sace.

 

Lamarin ya farune a karamar hukumar Hong ta jihar Adamawa.

 

‘Yan Bindigar sun je gidan mutumin me suna Bakomi Andrawus wanda kuma suka kasheshi suka sace diyarsa.

 

Da farko sun nemi a basu miliyan 2 kamin su saketa amma aka gaya musu 170,000 aka tara, suka kuma amince su karba, wajan karbar ne aka musu kofar rago aka bude musu wuta tare da kashe daya daga ciki.

Kakakin ‘yansandan jihar, DSP Sulaiman Nguroje ya tabbatar da faruwar lamarin.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *