fbpx
Saturday, April 17
Shadow

Yanda Gobara ta kama wani gida ta cinye yayin da masu gidan suka tafi Makaranta a Kano

Adaidai wannan lokaci gobara ta kama a wani bene mai hawa daya, da ke layin Malam Ibrahim Khalil da ke Rijiyar Zaki kudu da ke cikin birnin Kano.

 

Hutudole.com ta ruwaito cewa wutar ta kama ne a wani daki dake saman benen gidan, Makotan gidan sun tabbabatarwa da hutudole cewa mutanen gidan ba sa nan sun tafi Makaranta.

 

Gobarar bata dade da kamawa bane yan kwana-kwan dake rijiyar zaki suka kawo dauki inda sukai ta zuba ruwa.

 

Sai dai wutar ta na tsaka da ci ne yan kwanan kwanan na zuba ruwansu ya kare, bayan mintuna 15 ne sai ga motar kwana-kwana ta Gwamnatin tarayya inda ta cigaba da kashe wutar.

Wutar dai ta cinye dikkanin rufin dakunan da duk abinda ke cikin dakunan saman benen.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *