fbpx
Thursday, April 22
Shadow

Yanda gwamna Ganduje ya tsallake Rijiya da baya a wani hadarin jirgin sama da duka fasinjojin ciki suka mutu

Gwamna Jihar Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya bayar da labarin yanda ya tsallake Rijiya da baya a wani hadarin jirgin sama da duka mutanen ciki suka mutu.

 

Yace lamarin ya farune a Shekarar 1996, 20 ga watan Yuni a Jos, yace hadarinne ya rutsa da tsohon Gwamnan jihar na mulkin Soja, Abdullahi Wase.

 

Ya bayyana hakane yayin da Jakadar Najeriya a kasar Romania, Barr. Safiya Nuhu ta kai masa ziyara, inda yace mahaifinta na cikin wanda suka rasa ransu a wancan Lokaci.

 

Gwna Ganduje yace shima da dashi za’a yi tafiyar amma kuma ziyarar da wasu wakilan Gwamnatin tarayya zasu kai jihar Kano a wancan lokaci ya hanashi tafiyar, saidai daga baya suka saamu Labarin jirgin yayi hadari, Kamar yanda PMnews ta ruwaito.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *