fbpx
Tuesday, June 15
Shadow

Yanda IPOB ta yaudaremu mukawa membobinta horon yaki>>Wasu Korarrun Sojoji da aka kama

Wasu korarrun Sojoji 3 da aka kama sun bayyana yanda kungiyar IPOB ta musu alkawuran kyautata rayuwarsu amma ta kasa cikawa.

 

Korarrun Sojojin, Chinasa Orji, Godswill Steven, Linus Owalo, masu shekarun 35, 32, da 23 sun bayyana cewa, duk an koresu daga aikin soja ne bayan da suka nuna rashin Biyayya.

 

Sun kara da cewa, Nnamdi Kanu ya musu alkawarin biyansu nunkin Albashin da ake basu a aikin soja da kuma kaisu kasar waje su yi horo, sannan kuma ya gaya musu cewa idan ya kafa kasarsa ta Biafra, sune zasu zama manyan janarorinsa.

 

Matasan sun bayyana cewa IPOB ta basu 100,000 kowannensu wanda kuma suka amince suka je suka horar da mayakan IPOB da ake kira da ESN wanda yawansu ya haura 4,000.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *