fbpx
Saturday, October 16
Shadow

Yanda matashi ya kashe mahaifiyarsa saboda ta hanashi Abinci

An gurfanar da matashi, Solomon Ochadi dan shekaru 25 saboda kashe mahaifiyarsa, Elizabeth Ochadi a gaban kotu.

 

Lamarin ya faru ne a Ojo dake jihar Oyo.

 

Dansanda me gabatar da kara ya bayyana cewa matashin ya ture mahaifiyarsa jikin bangone wanda haka yayi sanadiyyar mutuwarta.

 

Yace matashin ya dawo daga gonane ya tarar babu abinci a gidan shine abin ya bata masa rai.

 

Ya haka rami dan binne mahaifiyar tasa amma daga bisani ‘yan uwansa suka kyankyasawa ‘yansanda lamarin.

 

An dai daga sauraren karar sai 23 ga watan Nuwamba.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *