fbpx
Tuesday, August 3
Shadow

Yanda Shugaban Sojojin Najeriya, Janar Farouk Yahaya yayi wa’azi a masallacin Juma’a

Yadda Shugaban Sojoji Na Kasa, Janar Faruk Yahaya Ya Koma Shehin Malami, Inda Ya Buge Da Wa’azi A Masallaci A Yayin Sallar Juma’a

…ku yada (sharing) domin duniya ta san cewa mun yi dacen Shugaban rundunar Sojoji Nagari a Nijeriya

Ko Kun san abunda ya faru jiya a Masallacin Juma’a Abuja?

Wallahi jiya a masallacin Juma’a (COAS General Faruku Yahaya) ya yi matukar farantamin rayuwa, ban taba tunanin Nijeriya za ta samu shugaba irin Malam Faruku ba a wannan zamanin.

Bayan an kammala sallar Juma’a Chief Of Army Staff General Faruk Yahaya ya karbe lasifika ya fara wa’azi akan zalunci da cin amana yana mai cewa:

Wannan duniyar bazamu tabbata aciki bah dole watarana zamu mutu ko munaso ko bamaso

Idan bakasan miye mutuwa ba za’a samu mahaifiyarka ta mutu, ko baban ka, ko matar ka, ko yayan ka, ko kawun ka, ko abokinka, ko malamin ka. Dole za’a samu wani dan uwanka yataba mutuwa.

Yanda kake ganin mutuwa yau taje wurin wannan gobe taje wurin wancen to tabbas watarana awurinka zatazo ko ka shirya ko baka shirya ba

Ita mutuwa bata jiran mutum sai ya shirya

Mutuwa wajibi ce ga kowane rai

Dukkan rayuwa mai mutuwa ce

Shugabannin siyasa nawa ne suka mutu a nigeria?? Wasu akan kujerar mulki mutuwa taje musu, wasu bayan sun gama mulki.

Yan kasuwa nawa ne suka mutu a nigeria??
Ga kudi da dukiya a banki, ga manyan gidaje na alfarma, ga manyan motoci na alfarma, ga masu gadi ta ko ina. Duk wannan bai hanasu mutuwa bah.

Jami’an tsaro nawa ne suka mutu a nigeria??
An kashe wasu a fagen daga, wasu sun mutu a gida wasu a assibiti.

Yan ta’adda nawa ne suka mutu a nigeria?

Yara nawa ne suka mutu a nigeria da matasa??

Malamai nawa ne suka mutu a nigeria??

Ita mutuwa alkawarin Allah ce dukkan rayuwa dole zata dan-dana mutuwa (Kullu nafsin za’ikatul maut Qur’an 3-185) (Surah Ankabut 57-59) ko kaso ko kaqi dole zaka mutu inji Allah Subhanahu wata’ala.

Dole akwai ranar alqiyama

Dole za’ayi hisabi

Dole za’a bada sakamako ko wuta ko aljannah

Duk abinda mutum ya aikata mai kyau ko marar sa kyau wallahi zai gani a wannan ranar, a ranar da bawani mai maka agaji ba mai ceton ka sai ayukan dakayi a duniya.

Quran Surah Zalzalah ayah 7-8(Faman Yaa mal misqala zarrathn khairan yarah, waman yaa mal misqala zarrathn sharran yarah).

Duk abunda mutum ya aikata mai kyau ko marar kyau zai gani a wannan ranar.

IDAN KASAN DA WANNAN KUMA KAYI IMANI DA RANAR ALKIYAMA

Me zai sa kayi zalunci?

Me zai sa kayi ta’addanci?

Me zai sa kaci amana?

Me zai sa ka kashe rayuwar bayin Allah da basuji ba basu gani bah?

Me zai sa kayi sata ko kidnapping?

Me zai sa ka sace dukiyar al’umma bayin Allah?

Me zai sa kahana mutane zaman lafiya?

Manzon Allah s.a.w yana fada a hadisi ingantacce cewa: duk wanda ya daga makami domin ya tada hankalin al’umma to baya tare damu.

Bakaso ka kasance tare da manzon Allah ne
Bakason Allah yayima rahama ne
Bakason Allah ya gafarta ma ne

To me zaisa ka dauke makami kana zubar da jinin bayin Allah??

Ahaka malam faruku yacigaba da wa’azi a wannan masallacin har sai da ya share awa daya (one hour)

Dukkan sojojin dake sallah awurin sukayi shuuu kamar an musu mutuwa. Wasu Sojojin sai zubar da hawaye sukeyi a wannan masallacin na (Mogadishu Contentment dake Abuja).

Daga karshe Malam Faruku yayi addu’a ga tsohon shugaban rundunar sojoji marigayi Gen. Ibrahim Attahiru sannan yayi Addu’a ga Wannan kasar tamu Nijeriya.

Allah ya bamu zaman lafiya a Nijeriya

Allah ya karo mana shugabanni masu imani masu ilimin addini irin General Faruku Yahaya.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *