fbpx
Wednesday, January 26
Shadow

Yanda Sojoji suka kashe mutane a kauyen Katsina saboda yin Zanga-Zanga kan matsalar tsaro

Wasu mazauna ƙauyen Kanon Haki da ke ƙaramar hukumar Funtua a jihar Katsina sun yi zargin cewa jami’an tsaron Najeriya sun kashe mutanen yankin biyu tare da jikkata wasu huɗu a lokacin wani harbin kan mai uwa da wabi.

Shaidu sun faɗa wa BBC cewa jami’an tsaron sun yi harbe-harben ne kan mutanen da suka rufe babban titin Funtua zuwa Gusau, yayin wata zanga-zangar nuna fushi kan wani harin ‘yan fashin daji da suka ce ya yi sanadin mutuwar mutum bakwai.

Mazuna kauyen sun kuma ce sun yi zanga-zanga ne saboda yadda jami’an tsaro suka ki kai mu su dauki har maharan suka gama cin karensu babu babbaka.

Wani uba ya shaida wa BBC cewa dansa na cikin wadanda jami’an tsaro suka jikkata, ya ce majinyacin yana cikin mawuyacin hali.

“Muna wajen zaman makoki ne, muna zaman makoki suka yi wannan harbin.”

Ya ce dan nasa na zaune tare da sautran jama’an da ke zaman makokin a kofar gidansa.

“Yana tare da mu a wajen da muka yi jana’izar wadannan mamatan bakwai.”

Ya ce dan nasa ma bai je wajen zanga-zangar ba samsam.

“An kashe mani kanina, an kashe mani dan wana, an kashe mani wan uwar shi, da kuma dan yata duka an kashe su. Muna zaune wajen makokin rashin wadannan mutanen tare da shi.”

Ya kuma bayyana halin da dan nasa yake ciki:

“Mun kawo shi asibiti. Akwai harbi a cinyarsa ta kafar hagu, an harbe shi har harsashin ya fita ta baya. Sai kuma kafar dama, saman tafin kafar inda suka harbe shi ta saman kafar kuma harsashin ya fita ta kasan kafar.”

Mahaifin wannan yaro ya kuma ce yayin da suke neman ma sa magani, sai jami’an tsaron suka bi su har asibiti inda suka yi kage cewa yaron dan ta’adda ne.

“Sai suka ce suna neman iyayen yaron, sai na ce musu gani. Sai suka ce ai wannan yaron dan ta’adda ne. Sai na ce musu da wanne za mu ji da shi? Barayi sun kashe mana mutum bakwai, ku kuma kun yi harbi har mun rasa wasu mutum biyu, ga mutum hudu kuma mun kawo asibiti.”

Ya kuma ce bayan da suka ga mummunan halin da suka saka wannan matashin har ta kai ga, “malaman asibiti na cewa sai an kai shi wani babban asibiti a Katsina, sai suka sabe kawai suka tafi.”

Wani mazunin garin na daban wanda shi ma yace ya rasa makusantansa a harin yayi zargin cewa har cikin garin jami’an tsaron suka shiga suna harbi.

“Bayan da muka ga jami’an tsaro sun ki kai mana dauki duk da rahoton da muka kai musu, shi ne muka fita kwanmu da kwarkwatarmu domin yin zanga-zangar nuna bacin rai.”

Ya ce su na cikin haka sai, “sojoji suka zo kuma duk da bamu da makamai amma sai sojojin suka rika harbinmu.”

BBC ta tuntubi rundunar ‘yan sandan jihar Katsina amma ba su amsa kiran da muka yi musu ba har aka hada wannan rahoton.

Daga BBChausa.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *