fbpx
Saturday, April 17
Shadow

Yanda Sojojin Najeriya suka yi zanga-zanga da harbi a Sama saboda rashin kulawa da rashin makamai masu kyau

Sojojin Najeriya a Maimalari dake Jihar Borno sun yi zanga-zanga da nuna rashin jin dadinsu bisa rashin kulawa da basu makamai masu kyau.

 

Hakan ya biyo bayan aika sojojin wani aiki da aka yi wanda kuma basu ji dadin hakan ba, kamar yanda Channelstv ta ruwaito.

 

Daya daga cikin sojojin ya bayyana rashin jin dadinsu akan wannan lamari inda yace a baya an gaba aika Tawagar sojoji zuwa Marte wadda kuma gaba dayansu suka mutu a hannun Boko Haram saboda sakaci.

 

Kakakin rundunar Operation lafiya dole,  Col Ado Isa ya tabbatar da faruwar lamarin inda yace amma an shawo kanshi.

 

A baya ne dai, hutudole.com ya ruwaito muku yanda me baiwa shugaban kasa shawara kan tsaro, Babagana Monguno yace ba’a san yanda aka yi da kudin makaman da shugaba Buhari ya bayar a siya ba

 

Saidai daga baya ya gyara maganar tasa.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *