Dakarun sojan Najeriya sun kashe mayaƙan Boko Haram guda 48 tare da ceto mutum 11 a Jihar Borno, a cewar mai magana da yawun rundunar.
Wata sanarwa da Birgediya Mohammed Yerima ya fitar a yau Asabar ta ce dakarun rundunar 28 a ƙarƙashin shirin Lafiya Dole sun kashe ‘yan bindiga tara a wata fafatawa a yankin Chibok zuwa Damboa.
Kazalika ya ce an ceto mutum uku da aka yi garkuwa da su tare da ƙwace bindigar AK-47 guda bakwai.
Ya ce dakarun nasu sun samu nasarar ce bayan samun bayanan sirri da ke cewa an ga mayaƙan na tserewa sakamakon luguden wutar da ake yi musu a Dajin Sambisa.
A wani kwanton ɓauna na daban, sojojin sun kashe ‘yan Boko Haram 39 a garin Askira sannan suka ceto mutum takwas da suka yi garkuwa da su.
Haka nan, sojoji sun sake yin nasarar ƙwato bindiga ƙirar AK-47 guda takwas.
Sai dai sanarwar ba ta bayyana lokacin da sojojin suka kai waɗannan hare-hare ba sannan kuma ko wani soja ya ji rauni ko rasa rai.
Amma ta ce ɗaya daga cikin mutanen da aka ceto ya ji rauni kuma yana kwance a asibitin sojoji.