fbpx
Saturday, October 16
Shadow

Yanda wani magidanci ya sha guba ya mutu saboda matarsa ta bata masa rai a Adamawa

Wani mutum me mata 1 da yara 3 ya sha guba ya mutu saboda bacin ran da matarsa ke sakashi ciki.

 

Vandu Weida dan shekaru 29 dake Mildu a karamar hukumar Madagali ta jihar Adamawa ya yi fada da matarsa.

 

Bayan fadan nasu ne sai yace ta isheshi, duniyar ma ta isheshi dan haka mutuwa kawai zaiyi.

 

Ashe da gaske yake sai ya je ya dauko guba ya kwankwada, nan aka ganshi kwance yana kakakin mutuwa, an garzaya dashi Asibiti inda acan ya karasa musutuwa.

 

Hukumar ‘yansandan jihar bata ce komai ba kan lamarin.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *