fbpx
Saturday, April 17
Shadow

Yanda Wani tsagera ya kai hari masallacin Makkah

Dakarun da ke lura da masallacin Makka sun kama wani mutum da ke dauke da wuka a harabar mmasallacin a yammacin ranar Talata.

Maimagana da yawun ‘yan sandan da ke lura da masallacin ya ce mutumin ya fado masallacin ne yana ihu yana nuna goyon bayansa ga kungiyoyin ‘yan ta’adda, bayan an idar da sallar La’asar a hawa na farko na masallacin mai tsarki.

“Nan da nan aka kama mutumin kuma za a dauki matakan shari’a da suka dace a kan shi,” in ji kakakin ‘yan sandan.

Shugaban limaman masalacin Sheikh Sudais ya ce, “Mutumin bai girmama muhimmancin wurin ba. Allah ya sanya masallacin ya zama wurin bauta, a yi sallah da ɗawafi da kuma aikin Hajji.”

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *