fbpx
Monday, November 29
Shadow

Yanda Wasu Kiristoci suka je wajan Maulidi a Kaduna

Kiristoci, ciki har da limamai sun taya Musulmi murnar zagayowar ranar haihuwar Annabi Muhammadu tsira da aminci su tabbata a gare shi, a Kaduna ranar Talata.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa mabiya addinan biyu sun taru a filin wasa na Ranchers Bees a tsakiyar birnin inda suka ce sun yi taron ne don karfafa zumunci da inganta hain kai.

Shugaban cocin Christ Evangelical Intercessory Fellowship Ministries na unguwar Sabon Tasha, Pastor Yohanna Buru wanda ya jagoranci wata tawagar Kiristoci ya ce ya halarci taron ne don murnar haihuwar Annabi.

Ya jaddada cewa “Annabi na kowa ne ba tare da la’akari da yare ko al’ada ko kalar fata ko nahiya ko yanki ba saboda ya yi kira ga zaman lafiya a gaba aya rayuwarsa.”

Ya kuma bayyana cewa a matsayinsa na mai son zaman lafiya kuma malamin addinin Kirista, halartar taron tare da Musulmai ba zai sauya masa addini ba.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

1 Comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *