fbpx
Tuesday, May 18
Shadow

Yanda wasu tsagera sukawa ‘yarsanda Tsirara a jihar Ondo

Wasu tsagera 4 sun tubewa wata ‘yarsanda kayanta suka mata tsirara a jihar Ondo.

 

‘yarsandar Me suna Bosede Ajayi na daga cikin wanda aka aika su binciki wani da yayi barazanar kisa.

 

Saidai da suka je binciken, an ci zarafinsu inda Shugaban tsagerun, Oladele Samuel ya bayar da umarnin a mata tsirara aka kuma daketa.

 

Kakakin ‘yansandan jihar, Bolaji Salami ya tabbatar da faruwar lamarin inda yace sun kama duka wanda ake zargi kuma da zara an kammala bincike za’a kaisu kotu.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *