fbpx
Thursday, April 22
Shadow

Yanda ‘Yan Bindiga suka kaiwa Tawagar Sojojin Najeriya harin kwantan Bauna da Kwace makamai da tsabar kudi Naira Miliyan 28

‘Yan Bindiga a jihar Benue, Sun kaiwa Tawagar Sojojin Najeriya harin Kwantan bauna inda suka sace tulin makamai da kudi da ake tsammanin sun kai Naira Miliyan 28.

 

Sojojin Na kan hanyar zuwa kai dauki ne kan rikice-rikicen kabilanci yayin da lamarin ya faru, kamar yansa hutudole.com ya samo muku daga rahoton people’s gazette.

 

Wata majiyar Tsaro ta bayyanawa majiyar tamu cewa, Sojojin na dauke da makamai da sauran kayan amfanine da za’a kaiwa Sojojin dake bakin daga yayin da ‘yan Bindigar suka musu Afke.

 

Sojojin sun tashi ne daga karamar Hukumar Katsina Ala zuwa Ojo yayin da lamarin ya faru. Majiyar tsaron ta bayyna cewa ba’a zargin sojojin da cin amana amma abin takaici ne ace tsagera da basu da wata kwarewar yaki sun ci karfin Sojoji.

 

Da aka aike da dakaru dan kaiwa Sojojin dauki, an tarar ba komai a wajan da aka kai musu harin, amma zuwa yanzu an fara bincike dan gano sojojin da suka bace.

 

Daga cikin sojojin da suka bace akwai me mukamin Kaftin, A.T Adedayo.

 

“Yes, the bandits stole weapons and also about N28 million from the soldiers,” the senior officer said. “The entire situation has been under investigation since the headquarters heard about it.”

 

The logistics team, led by A.T. Adedayo — an army captain — was reported missing, including a general-purpose machine gun and over 2,000 rounds of ammunition.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *