fbpx
Friday, May 14
Shadow

Yanda ‘yan kasuwar shanu suka bi ‘yansanda a guje, ‘yansandan sun tsere da tsira da rayuwarsu

An samu wani yanayi n matsalar tsaro a kasuwar shanu dake Enugu inda ‘yan kasuwar suka bi ‘yansanda da jami’an gwamnati da gudu.

 

Hakan ya farune bayan da ‘yansanda tare da wasu jami’an gwamnati suka je kasuwar da niyyar rusheta. Saida a cewar wai ganau ya bayyannawa Punchng cewa ‘yan kasuwar sun fito da bindigu suka bi ‘yansandan da gudu wanda suka tsere.

 

A karshe har kona motar ‘yansanda daya suka yi, kamar yanda Rahoton ya nunar.

 

An dai amince a rushe kasuwarne saboda matsalar tsaro, lura da yanda ta yi kusa da gidan gwamnatin jihar.

 

Kwamishinan’yansanda na jihar, Muhammad Aliyu ya tabbatar da faruwar lamarin inda yace abin be masa dadi ba, lura da cewa an samu fahimtar juna tsakanin gwamnatin da ‘yan kasuwar kamin fara maganar rusheta.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *