fbpx
Sunday, September 19
Shadow

‘Yansanda basu da yawan da zasu iya magance matsalar tsaro a Katsina>>Gwamna Masari

Gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari ya bayyana cewa, ‘yansanda basu da yawan da zasu iya magance matsalar tsaro a jihar.

 

Gwamnan ya bayyana hakane a ganawar da yayi da shugaban ‘yansandan Najeriya, IGP Alkali Usman Baba yayin ziyarar da ya kai masa.

 

Gwamnan yace yawan mutanen jihar Katsina ya kai Miliyan 8 amma ‘yansandan da ake dasu basubkai Dubu 3 ba.

 

Yace a ma yi kiyasin sun kai Dubu 3, to hakan na nufin kowane dansanda daya zai kula da mutane 200,000 ne, yace ta yaya aikinsa zai yi kyau?

 

Gwamnan ya kuma yi magana akan makaman da ‘yansandan ke rikew.

 

A nasa bangaren, shugaban ‘yansandan, ya bayyana cewa, zasu dauki mutane 20,000 aiki kamar yanda shugaban kasa yayi Umarni.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *