fbpx
Wednesday, June 23
Shadow

‘Yansanda sun tsinci karamin yaron da wata mata ta yadda ta tsere a jihar Yobe

Wata mata ta yadda karamin yaro dan shekara 1 ta tsere a jihar Yobe. Lamarin ya farune a yankin Nyanya dake Damaturu na jihar.

 

Kakakin ‘yansandan jihar, Dungus Abdulkarim ya tabbatar da faruwar hakan. Yace wata mata ce ta je da yaron ta baiwa wani Almajiri tace ya kaiwa Mamman Farouk a wani gida.

 

Saidai ashe dabara ce ta shirya dan ta yadda yaron, inda aka nemeta ko sama ko kasa aka rasa. Yace suna kira ga jama’a su taimaka wajan gano iyayen yaron.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *