fbpx
Saturday, October 16
Shadow

‘Yansandan Najeriya ta daura damara bayan kisan Janar Souleimani na Iran

Babban Sufetan ‘yan sandan Najeriya, Mohammed Adamu ya umarci jami’ansa da su kasance cikin shirin ko-ta-kwana a sassan kasar sakamakon wasu bayanai da ke da nasaba da kisan da Amurka ta yi wa Janar Qassem Souleimani na Iran.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

A cikin wata sanarwa da ya fitar, mai magana da yawun rununar ‘yan sandan Najeriya, Frank Mba ya ce, sun samu bayanan sirri da ke cewa, wasu mutane na shirin tayar da kura ko kuma yin zagon kasa ga Najeriya biyo bayan kisan Souleimani.

Sanarwar ta ce, an umarci mataimakan babban sufetan ‘yan sandan kasar da sauran kwamishinonin ‘yan sanda da su tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin al’umma a sassan kasar.

Babban Sufetan ya lashi takobin bayar da tsaro ga ‘yan Najeriya da kuma baki da ke rayuwa a kasar, yayin da ya gargadi masu tayar da kayar baya da su kauce wa fantsama kan tituna.

Kisan da Amurka ta yi wa Janar Souleimani ya tunzira jama’a gudanar da zanga-zanga a birnin Tehran da wasu kasashen yankin gabas ta tskiya a ranar Juma’a, yayin da rahotanni ke cewa, mabiya akidar shi’a sun gudanar da makamanciyar wannan zanga-zanga a birnin Abuja na Najeriya.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *