fbpx
Thursday, December 2
Shadow

Yanzu haka an kai Nnamdi Kanu kotu za’a ci gaba da shari’a

Rahotanni daga babban birnin tarayya, Abujq na cewa, An kai shugabab haramtacciyar kungiyar IPOB dake son kafa kasar Biafra,  Nnamdi Kanu kotu dan ci gaba da shari’ar da ake masa.

 

Saidai an hana ‘yan jarida shiga babbar kotun gwamnatin tarayyar dake Abuja.

 

A baya dai, Kungiyar IPOB ta yi gargadin cewa, idan ba’a gabatar da Nnamdi Kanu a kotu ba a yau, to zata durkusar da tattalin arzikin jihohin Inyamurai.

 

Kanu ya samu rakiyar tsohon gwamnan jihar Anambra da Lauyoyinsa amma an hana sauran lauyoyi da ‘yan jarida shiga wajan shari’ar.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *