fbpx
Monday, October 25
Shadow

Yanzu-yanzu: Gwamna Ganduje ya nada Aliyu Ibrahim-Gaya a matsayin sabon sarkin Gaya

Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano da sanyin safiyar Lahadi ya nada Alhaji Aliyu Ibrahim-Gaya a matsayin sabon sarkin Gaya.

Ibrahim-Gaya ya gaji mahaifinsa marigayi, Alhaji Ibrahim Abdulkadir wanda ya rasu yana da shekaru 91 bayan doguwar jinya.

Sakataren Gwamnatin Jiha, Alhaji Usman Alhaji ya sanar da nadin a madadin Gwamna.

Usman Alhaji ya kara da cewa; Nadin ya biyo bayan shawarwarin da masu nadin sarautar masarautar Gaya suka gabatar bayan gabatar da ‘yan takara uku, inda Gwamnan ya amince da nadin Aliyu Ibrahim Gaya a matsayin sabon Sarkin Gaya.

Masu zaben sarkin sun hada da, Alhaji Usman Alhaji (jagoran masu yin sarkin), Wada Aliyu (Madakin Gaya), AIG Alhaji Bashir Albasu (Makaman Gaya), Alhaji Jafar Usman (Turakin Gaya).

Idan zaku tuna masarautar Gaya na daya daga cikin sabbin masarautu hudu da gwamnatin Gwamna Ganduje ta kirkiro a shekarar 2019.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *