fbpx
Saturday, October 16
Shadow

Yanzu -yanzu: Kotu ta umarci Gwamnatin Tarayya da ta biya Sunday Igboho diyyar N20b

Wata Babbar Kotun Jihar Oyo, da ke Ibadan ta umarci Gwamnatin Tarayyar Najeriya da ta biya diyya ga Sunday Adeyemo, wanda aka fi sani da Igboho, kan zunzurutun kudi har N20billion kan barnar da akayi mai a lokacin da jami’an tsaro suka gidansa.

Idan zaku tuna jami’an tsaro sun mamaye gidan Igboho da ke Ibadan don neman makamai a cikin sa’o’i masu yawa, inda suka kashe mutane biyu tare da kame wasu abokan sa.

An dakatar da yunkurin Igboho na tserewa daga kasar a Jamhuriyar Benin, inda ake tsare da shi kuma ake zarginsa da kin bin umurnin gwamnatin Najeriya.

Lauyan sa ya je kotu don kalubalantar jami’an tsaro na farin kaya kan cin zarafinsa da kuma yi masa barna a gidansa.

Cikakkun bayanai na nan tafe…..

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *