fbpx
Saturday, April 17
Shadow

Yanzu-Yanzu: Majalisar Dattawa ta tabbatar da nadin sabbin Shugabannin Hafsosin Sojojin Nageriya

Majalisar Dattawa ta tabbatar da nadin sabbin Shugabannin Hafsosin Sojojin Nageriya.

Hafsosin sun hada da Chief of Defence Staff, Manjo-Janar Leo Irabor, Chief of Air-Marshal Isiaka Oladayo Amao, Chief of Naval Staff Rear Admiral Awwal Zubairu Gambo, Chief of Army Staff General Ibrahim Attahiru.

Bayan tabbatarwa a ranar Talata, Shugaban Majalisar Dattawa Ahmad Lawan ya shawarci sabbin hafsoshin sojojin da su jajirtace wajen yaki da masu tayar da kayar baya, yan bindinga da‘ yan fashi a duk Inda suke a fadin kasar nan.

Ya kuma tunatar da su da su cewa, yan Najeriya na tsammanin abubuwa da yawa daga gare su don magance matsalolin tsaro da kasar ke fuskanta.

Tabbacin nasu ya zo ne mako guda kacal bayan Majalisar Wakilai ta tabbatar da nadin nasu.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *