fbpx
Tuesday, August 3
Shadow

Yanzu-Yanzu: Sheikh Abduljabbar Kabara bashi da lafiya sosai, yana zubar da Jini a gidan yari

Rahotanni daga jihar Kano na cewa, Sheikh Abduljabbar da aka kama a Kano saboda yiwa fiyayyen halitta, Annabi Muhammad (SAW)batanci, bashi da lafiya.

 

Rahoton na Sahara Reports yace Abduljabbar na zubar da Jini ta Dubura.

 

Lauyan Abduljabbar, Rabiu Abdullahi ne ya bayyana haka inda yace likitan gwamnati ya tabbatar da rashin lafiyar ta Abduljabbar.

 

An duba malamin sannan aka bashi magani. Da aka tambayi lauyan ko suna zargin akwai wani abu da ake aikatawa ba daidai ba ko ana son kashe malaminne? Sai ya kada baki yace ko da suna zargin hakan basu da hujja, yace amma dai suna son sanar da Duniya abinda ake ciki ne.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *