fbpx
Monday, September 27
Shadow

Yanzu-Yanzu: Shugaba Buhari yayi sabbin nade -nade

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da nadin sabbin manyan shuwagabannin wasu hukumomi a karkashin ma’aikatar ilimi ta tarayya.

An kaddamar da nade -naden ne a ci gaba da kokarin da gwamnatin tarayya ke yi na kara karfafa harkar ilimi a kasar nan.

An sanar da nade -naden ne a cikin wata sanarwa dauke da sa hannun Mista Bem Goong, Daraktan yada labarai da hulda da jama’a na ma’aikatar, kuma an bai wa manema labarai a Abuja ranar Laraba.

Ya lissafa sabbin wadanda aka nada a matsayin: Farfesa Akpama Ibar a matsayin Babban Sakatare, National Commission for Mass Literacy, Adult And Non-Formal Education; Farfesa Chinwe Anunobi, Darakta/Shugaba, Laburaren Kasa (dakin karatu); da Farfesa Musa Maitafsir a matsayin Darakta/Shugaba, Cibiyar Malamai ta Ƙasa.

Goong ya kara da cewa shugaban ya kuma amince da sake nada Magatakarda/Babban Darakta, Kwamitin Rajistar Malamai na Najeriya (TRCN), Farfesa Josiah Ajiboye, a wa’adi na biyu kuma na karshe na shekaru biyar, daga ranar 1 ga watan Agusta.

Hakazalika, an sake nada Farfesa Bashir Usman a matsayin Babban Sakatare, Hukumar Kula da Ilimin Noma ta Kasa, a wa’adi na biyu kuma na karshe na shekaru biyar.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *